Kim Jong Un da Putin za su halarci bikin cika shekaru 80 da kawo ƙarshen Yaƙin Duniya na Biyu a China
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, da shugaban Rasha, Vladimir Putin, za su kasance cikin manyan shugabanni da za su halarci babban bikin soji da za a yi a Beijing, babban birnin kasar China, domin tunawa da cika shekaru 80 da ƙarshen Yaƙin Duniya na Biyu.
Bikin, wanda za a gudanar a Dandalin Tiananmen, zai samu halartar shugabanni 26 daga sassan duniya, ciki har da shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, shugaban Belarus, Alexander Lukashenko, da shugaban kasar Indonesia, Prabowo Subianto. Wannan taron ya kuma dace da zagayowar ranar 3 ga Satumba, wacce aka ayyana a matsayin ranar da Japan ta mika wuya ga ƙasashen kawance a shekarar 1945.
Shugaban kasar Sin, Xi Jinping, shi ne zai jagoranci bikin, inda ake sa ran zai nuna ƙarfi da ci gaban fasahar sojin kasar, ciki har da sabbin makaman zamani. Duk da cewa babu yawancin shugabannin kasashen yammacin duniya da za su halarta, ana ganin wannan taron zai kara nuna ƙarfin dangantaka tsakanin Rasha, China da Koriya ta Arewa.
Alaka tsakanin waɗannan ƙasashe uku ta ƙara karfi tun bayan mamayar Rasha a Ukraine a 2022. China na ci gaba da tallafawa tattalin arzikin Rasha ta hanyar sayen makamashinta da kuma samar da fasahar zamani, yayin da Koriya ta Arewa ke tura makamai da ma’aikata domin goyon bayan rundunar Rasha.
Xi, Putin, da Kim ana sa ran za su kasance a tsakiya a lokacin parade ɗin, abin da ke iya nuna wata sabuwar garkuwa ta siyasa da soja tsakanin ƙasashen.