Ƙungiya Ta Nemi ECOWAS Ta Ɗauki Hausa A Matsayin Harshe Na Kasuwanci
Shugaban shirya bikin Ranar Hausa ta Duniya (World Hausa Day), Abdulbaqi Jari, ya yi kira ga Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) da ta ɗauki Hausa a matsayin harshe na kasuwanci da hulɗar zamantakewa a ƙasar baki ɗaya.
Jari ya bayyana hakan ne a taron manema labarai kafin bikin bana na Ranar Hausa ta Duniya da za a gudanar ranar Talata, 26 ga Agusta, 2025, a fadar Sarkin Daura. Ya ce amfani da Hausa zai ƙarfafa harkokin kasuwanci da haɗin kan al’ummomin Yammacin Afirka.
Ya kuma ce Hausa na da cikakken matsayi saboda yaduwar sa a ƙasashen Afirka fiye da 25, don haka zai iya zama harshen haɗin kai da cinikayya.
Jari ya bukaci gwamnatin tarayya ta amince da Hausa a matsayin harshe na ƙasa a Najeriya, yana mai cewa Hausa ta zama harshen Afirka mafi yaduwa kuma ta shiga cikin harsuna 11 da aka fi magana da su a duniya.