Kada Ku Zabi Mahaifina – In Ji ’Yar Shugaban Kamaru Paul Biya

A yayin da Kamaru ke shirin gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 12 ga Oktoba 2025, wata magana mai zafi ta fito daga cikin gidan shugaban kasar kansa. Brands Biya, ’yar shugaban Kamaru mai shekaru 92, Paul Biya, ta fito fili a shafinta na TikTok tana kira ga ’yan kasar da su guji sake kada wa mahaifinta kuri’a.

A cikin faifan bidiyon da ta wallafa, Brands ta bayyana cewa Kamaru na cikin mummunan hali na siyasa da tattalin arziki, kuma lokaci ya yi da a ba dan takarar bangaren adawa dama domin kawo sauyi. Wannan kalami nata ya tayar da kura a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama ke bayyana mamaki da kuma goyon baya, yayin da wasu kuma ke ganin hakan cin mutunci ne ga mahaifinta.

Paul Biya, wanda ya shafe kusan shekaru 42 a mulki, shi ne shugaban kasa mafi dadewa a nahiyar Afrika da ke kan karaga. Duk da shekarunsa da kuma tsawon lokacin mulki, shi ne har yanzu ke neman tazarcen mulki a karo na gaba. Wannan ya jawo cece-kuce a cikin gida da wajen kasar, inda ake ganin lokaci ya yi da ya mika ragamar mulki.

Kiran daga ’yar sa zai iya yin tasiri ga ra’ayin jama’a, musamman matasa da ke yawan amfani da kafafen sada zumunta. A yanzu dai idanu na kan ranar zaben domin ganin ko wannan kalami zai canza sakamakon siyasar kasar.

✍️ GW Hausa

Popular posts from this blog

Juyin Mulki Na Ci Gaba A Benin Republic, Sojoji Sun Kai Hari Gidan Shugaba Talon, Sun Kwace Talabijin Na Ƙasa.

Malema Ya Nemi Shugaban Ɗaya, Kuɗi Ɗaya Da Afirka Ba Tare Da Iyaka Ba

Uganda: Zaben ‘Yan Uwa a Majalisar Dokoki Na Kara Karbuwa Al’umma Sun Mayar da Siyasa Gado?