NATO Ta Tare Jiragen Rasha da Suka Keta Samaniyar Estonia

Hukumomin Estonia sun tabbatar da cewa jiragen yaki guda uku na Rasha, nau’in MiG-31, sun keta samaniyar kasar a ranar 19 ga Satumba 2025.

Rahotanni sun bayyana cewa jiragen sun shiga ne ba tare da flight plan ba, sun kashe transponders, kuma basu yi mu’amala da hukumomin zirga-zirgar jiragen sama na Estonia ba. Wannan ya faru ne a kusa da Tsibirin Vaindloo da ke cikin Gulf of Finland.

A cewar gwamnatin Estonia, wannan ketarewa ta dauki tsawon mintuna 12, wanda ya sanya NATO ta aika da jiragen F-35 daga Italiya domin tarwatsa su.

Bayan lamarin, Estonia ta kira Jakadan Rasha don nuna rashin jin dadin ta. Haka kuma, ta bukaci tattaunawa karkashin Article 4 na NATO, wanda ke bai wa kasashe memba damar gabatar da bukatar shawarwari idan akwai barazanar tsaro.

Hukumomin kasar sun bayyana cewa wannan danyen aiki daga Rasha na iya kara jefa yankin cikin tashin hankali, musamman ganin yadda rikicin Ukraine ke ci gaba da rikita tsarin tsaro a Turai.

GW Hausa

Popular posts from this blog

Juyin Mulki Na Ci Gaba A Benin Republic, Sojoji Sun Kai Hari Gidan Shugaba Talon, Sun Kwace Talabijin Na Ƙasa.

Malema Ya Nemi Shugaban Ɗaya, Kuɗi Ɗaya Da Afirka Ba Tare Da Iyaka Ba

Uganda: Zaben ‘Yan Uwa a Majalisar Dokoki Na Kara Karbuwa Al’umma Sun Mayar da Siyasa Gado?