Christopher Musa Ya Karɓi Rantsuwa Bayan Murabus ɗin Badaru

A yau, 4 ga Disamba 2025, tsohon Chief of Defence Staff (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa (rtd.), ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon Ministan Tsaro na Najeriya. Wannan na zuwa ne bayan murabus da tsohon ministan tsaro, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi a makon da ya gabata.

Mai magana da yawun Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Bayo Onanuga, ya tabbatar da nadin tare da fitar da hoton rantsuwar da aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa Abuja. Sunan Janar Musa ya isa majalisar dattawa tun bayan murabus ɗin Badaru, kuma majalisar ta tabbatar da shi bayan tsauraran tambayoyi da aka yi masa na tsawon awa biyar.

Janar Musa ya yi ritaya daga rundunar soja a watan Oktoba 2025 bayan kammala wa’adinsa a matsayin CDS, inda ya jagoranci rundunonin tsaro wajen yaki da ta’addanci a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma. Yana daga cikin manyan hafsoshin da suka yi fice a tarihin rundunar sojin ƙasa, kuma ya samu Colin Powell Award a shekarar 2012 saboda bajintar aiki.

An haife shi a Sokoto a 1967, kuma ya fara koyon soja a NDA a 1986. Ya yi aiki a matsayin:

Kwamandan 73 Battalion

GSO 1 Training & Operations

AD Operational Requirements

Infantry Representative, HQ Armour Corps
da sauran mukaman manyan jagoranci.


Nadin nasa ya jawo cece-kuce a kafafen yada labarai, inda wasu suka yaba da kwarewarsa, wasu kuma ke kallon wannan a matsayin sabon tsari wajen farfado da harkokin tsaro a Najeriya.

Zeeshan Amar 
GW Hausa 

Popular posts from this blog

Juyin Mulki Na Ci Gaba A Benin Republic, Sojoji Sun Kai Hari Gidan Shugaba Talon, Sun Kwace Talabijin Na Ƙasa.

Malema Ya Nemi Shugaban Ɗaya, Kuɗi Ɗaya Da Afirka Ba Tare Da Iyaka Ba

Uganda: Zaben ‘Yan Uwa a Majalisar Dokoki Na Kara Karbuwa Al’umma Sun Mayar da Siyasa Gado?