Malema Ya Nemi Shugaban Ɗaya, Kuɗi Ɗaya Da Afirka Ba Tare Da Iyaka Ba
Shugaban jam’iyyar Economic Freedom Fighters (EFF) na Afirka ta Kudu, Julius Malema, ya yi kira da a haɗa Afirka gaba ɗaya ƙarƙashin shugaba guda, kuɗi guda, majalisa guda da kuma rundunar soji guda.
Malema ya yi wannan kira ne a taron shekara na Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) da aka gudanar a Enugu, inda ya ce lokaci ya yi da shugabannin Afirka su yi watsi da iyakokin da Turawan mulkin mallaka suka bari.
Ya ce Afirka na da albarkatu da za su iya ƙarfafa tattalin arzikin duniya, kuma dole nahiyar ta dogara da kanta wajen samar da ci gaba. Malema ya kuma yi kira da a kawar da tsarin neman visa tsakanin ƙasashen Afirka domin sauƙaƙa hulɗa da haɗin kai.
Shugaban EFF ɗin ya yabawa Najeriya saboda rawar da ta taka wajen kawo ƙarshen wariyar launin fata (apartheid), inda ya ce Najeriya da Afirka ta Kudu za su iya jagorantar ci gaban masana’antu da cinikayyar nahiyar.
Game da matsalar ƙiyayya ga baƙin haure (xenophobia), Malema ya ce hakan cin amanar haɗin kan Afirka ne, yana mai jaddada cewa: “Afirkawa dole su so kansu, ba su kashe juna ba.”