Sojojin Najeriya Sun Musanta Rahoton Juyin Mulki da Soke Bukin ’Yancin Kai

Hedikwatar Tsaron Najeriya (DHQ) ta karyata rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa soke bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai na ƙasar yana da nasaba da yunkurin juyin mulki.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Rundunar, Brigediya Janar Tukur Gusau, ya fitar a ranar Asabar, DHQ ta bayyana rahoton a matsayin “karya tsantsa”, tana mai cewa manufarsa ita ce tada hankalin jama’a da haifar da rudani a cikin ƙasa.

Gusau ya bayyana cewa soke bikin ya biyo bayan shirin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na halartar taro mai muhimmanci a ƙasashen waje, tare da bai wa rundunar tsaro damar mayar da hankali kan yaƙin da ta ke yi da ta’addanci, ’yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya a sassan ƙasar.

Hedikwatar ta kuma ce binciken da ake yi kan wasu hafsoshin soja 16 ba shi da nasaba da wani yunkurin juyin mulki, illa dai mataki ne na cikin gida domin tabbatar da ladabi, da bin doka a rundunar soji.

DHQ ta roƙi ’yan Najeriya da su guji yarda da labaran ƙarya, tana mai jaddada cewa rundunar sojin ƙasar na da cikakken biyayya ga kundin tsarin mulki da gwamnatin Shugaba Tinubu, tare da tabbatar da cewa demokiradiyya ta dore a Najeriya.

GW Hausa

Popular posts from this blog

Juyin Mulki Na Ci Gaba A Benin Republic, Sojoji Sun Kai Hari Gidan Shugaba Talon, Sun Kwace Talabijin Na Ƙasa.

Malema Ya Nemi Shugaban Ɗaya, Kuɗi Ɗaya Da Afirka Ba Tare Da Iyaka Ba

Uganda: Zaben ‘Yan Uwa a Majalisar Dokoki Na Kara Karbuwa Al’umma Sun Mayar da Siyasa Gado?